El-Rufai ya ce za a kwashi gawar masu shisshigi a zaben Najeriya

El-RufaiHakkin mallakar hotoFACEBOOK/KADUNA STATE GOVERMENT
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce za a kwashi gawar duk dan kasar wajen da ya tsoma baki a zaben Najeriya na 2019.
El-Rufai ya bayyana haka ne ranar Talata da daddare a shirin Tuesday Live da fitaccen dan jaridar nan Cyril Stober ke gabatarwa a gidan talbijin na kasa NTA.
Gwamnan na jihar Kaduna ya yi wannan tssokaci ne mako guda bayan gwamnatin Najeriya ta zargi wasu kasashen waje, cikinsu har da Amurka da Birtaniya, da yunkurin tsoma baki a zaben kasar bayan sun nuna damuwa kan dakatar da alkalin alkalan kasar Walter Onnogen
"Muna jiran mutanen da ake kira su zo su tsoma baki a Najeriya, domin kuwa za su koma kasashensu a jakunkunan gawa," in ji Gwamna El-Rufai.
Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya na kokarin gudanar da harkokin kasa kamar yadda suka kamata, yana mai cewa su kansu kasashen waje sun sha fuskantar matsaloli kafin su kai matakin da suke a yanzu.
Gwamnan na jihar Kaduna dai ya sha yin irin wadannan kalamai da ke janyo ce-ce-ku-ce.
Duk sanatan da ya zo ku yi masa aski - El-Rufa'i
A shekarar 2018, ya nemi jama'a da su far wa sanatoci uku da suka fito daga jihar.
Gwamnan ya zargi Sanatocin da suka hada Shehu Sani da Suleiman Hunkuyi da Danjuma Laah, da hada baki domin hana majalisar dattawan Najeriya amincewa da bukatarsa ta cin bashi daga Bankin Duniya.
Nasir Ahmad el-Rufai ya ce "wadannan dattijan [sanatocin Kaduna] banza ne... domin su makiyan jihar Kaduna ne, ba sa son ci gaban jihar."
Sannan ya yi kira ga magoya bayansa da su askewa sanatocin gashin kansu da gemunsu domin a cewarsa "ba sa kaunar jihar."
BBC HAUSA
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post