Tsarin Trade Moni salon sayen kuri'ane da wayau>>Transparency International

Tsarin Trade Moni salon sayen kuri'ane da wayau>>Transparency International

Kungiyar kula da rashawa da cin hanci ta Transparency International ta bayyana cewa tsarinnan na Trade Moni da gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ke bayarwa ga kananan 'yan kasuwa a Najeriya sayen kuri'ane da wayau.



Shugaban kungiyar, Awwal Rafsanjani ne ya bayyana haka a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels, Awwal ya bayyana cewa tsarin sayen kuri'ane da wayau inda gwamnatin tarayya ke amfani da kudin baitilmani tana bayarwa.

Yace dalilinsu na cewa haka shine cikin shekaru 3 da suka gabata karkashin mulkin APC bata kawo wannan tsari ba sai ana gab da yin zabe, ya kara da cewa koda kuwa ba salon sayen kuri'a bane da wayau dole Duniya zata kalleshi a haka.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post