Shekaru Goma (Kenan Atiku Abuakar Yana Daukar Nauyin Ciyarwa A Masallacin Makkah Da Madina>>Almustapha Bin Abdallah Al-Aradhy
Wani bawan Allah daga garin Makkah ta Kasar Saudia, mai Suna Almustapha
Bin Abdallah Al-Aradhy wanda kuma ma'aikaci ne a masallacin Haramin
Makka yace yau shekaru Goma kenan Alhaji Atiku Abubakar yana daukar
nauyin ciyar da miliyoyin al’ummar musulmi a Haramin Makka da Madina a
yayin aikin Hajji da Umrah a kasar Makka.
Almustapha ya wallafa wannan bayani ne a shafin sa na Twitter a ranar 6 ga watan Janairun 2019.
Almustapha Al-Aradhy yace :- "Ina farin ciki tare da godiya ga Allah da
ya nuna mun wani bawan Allah daga kasar Najeriya mai Suna Atiku
Abubakar, wanda kuma shine mutum da ya tilo daga kasashen Afirika wanda
yake daukar nauyin ciyar da miliyoyin musulmi a Haramin Makkah da
Madina”.
Da yake zantawa da wakilin Saudi Gazette ta wayar tarho, Almustapha Bin
Abdallah Al-Aradhy yace “Na san Atiku Abubakar ne a Haramin Makka tun a
shekarar 2009 lokacin da ya fara daukar nauyin ciyar da al’umma a
lokacin bude baki na watan Ramadan, da masu Azumin Litinin da Alhamis,
kasancewar shi Atiku mutum ne mai yawaita Azumin Litinin da Alhamis a
kowani mako”.
“Tabbas wannan bawan Allah Atiku ya cancanci na yaba masa kasancewar sa
mutum daya tilo daga Afirika da yake daukar nauyin ciyarwa a masallacin
Haramin Makka da Madina.” A cewar Almustapha Bin Abdallah Al-Aradhy.
Rariya.