Salah ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afrika sau biyu a jere
Tauraron dan kwallon kafar kasar Egypt me bugawa kungiyar Liverpool
wasa, Mohamed Salah ya sake lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afrika sau
biyu a jere.
Mohamed Salah ya doke abokan takararshi da suka nemi wannan kyauta tare,
dan wasan Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang da abokin wasanshi a
Liverpool, Sadio Mane, Ya lashe gasarne a bikin da akayi a yau, Talata a
Dakar.