RAN MAZA YA BACI, 'YAN TA'ADDA KUN SHIGA UKU: Buratai ya jagotanci sojin kundumbala yaki da Boko Haram
Shugaban sojojin Nigeria Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai mai
dala'ilun yaki, ya jangoranci kaddamar da hari da kanshi akan 'yan
ta'addan Boko Haram a sassan jihohin Borno da Yobe wanda aka samu
nasaran hallaka 'yan ta'adda sama da dari kamar yadda rundinar sojin
Nigeria ta bayyana
Wannan hoton da ake gani na Janar Buratai tsohon hoto ne kusan shekaru
uku lokacin da yake ziyartar dakarun mayakan sojoji dake fagen yaki a
cikin jejin Sambisa, to a halin yanzu, kuma a halin da ake ciki; da
kanshi yake jagorantar sojojin kundunbala wajen kaddamar da hari akan
'yan ta'addan Boko Haram
Rundinar sojin Nigeria tace yanzu haka dakarun mayakan sojin Nigeria sun
kara kaimi ta yankin tabkin chadi don ganin sun murkushe duk wani
barazana na 'yan ta'adda a yankin tare da taimakon jiragen yakin sojojin
saman Nigeria, kuma wannan hari na musamman da ake kaddamarwa shugaban
sojoji Janar Buratai yake jagoranta da kanshi
Baba Buratai muna matukar godiya bisa ga wannan sadaukarwa da kayi
garemu 'yan Nigeria domin mu tsira da rayukan mu, hakika ka cancanci
yabo da godiya, muna nan muna ta hayaniya hankali kwance a gidajenmu,
shi kuma yana can cikin jeji yana fafatawa da 'yan ta'adda, amma duk da
haka wani katon banza sai ya buda baki yace dakarun mu wai basa yin
komai
Yaa Allah Ka taimaki shugaban sojojin Nigeria tare da rundinarshi Ka tabbatar musu da nasara akan 'yan ta'adda Amin
Datti Assalafiy.