Obasanjo Tsohon Najadu Ne Kuma Munafukin Allah Ta'ala>>Malam Bello Yabo

Obasanjo Tsohon Najadu Ne Kuma Munafukin Allah Ta'ala>>Malam Bello Yabo

Shahararren Malamin addinin Musulunci Malam Bello Yabo na jihar Sakkwato wanda aka san shi da rashin tsoro yayin Wa'azi ya kira Obasanjo a matsayin Tsohon Najadu kuma Munafukin Allah. 


"Ga wani tsohon Najadu can ya rubuta takarda da ya ke ba ita ce ta farko ba, ba wani shugaba da bai rubutawa wannan takarda ba. Ba magani nai illa Abacha. Abacha shi yai magani nai. Da ya rubuta Abacha irin ta sai ya sa aka murkushe shi aka jefa Shege gidan yari. Ku fada min duk shugaban kasar da aka yi akwai wanda yayi tabargazar da yayi a Najeriya?

Amma wai shi ya rubuta takarda ya tona asiri. Asirin wa? Yana saman Mulki da nai ya kai shi kara ya ce ya na lalata da mata nai. An yi ko ba a yi ba? Sun haifi 'ya'ya biyu ya ce kotu ta sa a yi bincike yana zargin ba na sa ba ne na Baban sa ne. Ko kun manta? To wai ka rubuta takarda wai wani bai iya mulki ba.
Daga Maje El-Hajeej Hotoro 

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post