Mazaje na rububin auren matar da mijinta ya sake ta saboda tace Buhari zata zaba

Mazaje na rububin auren matar da mijinta ya sake ta saboda tace Buhari zata zaba

Ga dukkan alamu matarnan da mijinta ya saketa dalilin dagewa da ta yi akan sai ta zabi shugaban kasa, Muhammadu Buhari a zabe me zuwa ba zata yi kwantai ba domin kuwa yanzu haka an samu mazaje sun yunkuro da cewa zasu aureta, duk da cewa dai wasu sun bayyana rashin kyautawar abinda ta wa mijin nata da shima hukuncin da ya dauka.



Babban masoyin Shugaban Kasa a jihar Kano Auwal G Danbarno ya sha alwashin auren matar da mijinta ya sake saboda ta dage sai ta zabi Buhari. 

Ya wallafa a shafinsa na facebook cewa, "Zan aureta ko ta kai shekaru Ɗari, kuma ko kuturwa ce. Matar da mijinta ya sake ta kan zaɓen Buhari"

Haka kuma shima wani da yake bayyana ra'ayinshi akan labarin da BBC suka wallafa ya bayyana cewa a shirye yake ya auri matar idan ta kammala Idda.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post