INEC ta ce Oby ta makara: Sai an yi zabe da ita

INEC ta ce Oby ta makara: Sai an yi zabe da ita

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC ta ce 'yar takarar shugabancin kasar a jam'iyyar ACPN Obiageli Ezekwesili ta makara wajen janye takararta a zaben 2019.


Mai magana da yawun hukumar, Malam Aliyu Bello ya ce sashe na 35 na dokar zabe ta shekarar 2010, ya nuna cewa jam'iyya ko dan takara zai iya janye takararsa kwanaki 45 kafin ranar da za a kada kuri'a.

Ya ce a zaben 2019, hukumar INEC ta ware 17 ga watan Nuwamba a matsayin rana ta karshe da 'yan takarar shugabancin kasa da na majalisar za su iya janyewa.


Malam Aliyu ya ce tanadin dokar shi ne idan dan takara ya yi niyyar janyewa daga takararsa, sai ya ankarar da jam'iyyarsa ta hanyar rubuta wasika inda ita kuma jam'iyyar za ta sanar da hukumar zaben.

Ya ce jam'iyyar ACPN ba ta sanar da hukumar INEC ba a kan lokaci, don haka hukumar za ta ci gaba da shirye-shiryenta na zabe yadda ya kamata.

Oby Ezekwesili dai ta janye daga takarar shugabancin Najeriya bayan da ta wallafa wasu jerin sakonni a shafinta na Twitter.

Tsohuwar mataimakiyar shugaban babban bankin duniyar, ta ce ta dauki matakin ne bayan ta tattauna da abokan shawarta na ciki da wajen kasar.

A cewarta, yanzu za ta mayar da hankali ne wurin shiga gamayyar jam'iyyun da za su kwace mulki daga jam'iyyar APC ko kuma su hana jam'iyyar PDP cin zabe.
BBChausa.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post