Majalisar tarayya ta tabbatar da dubu 30 mafi karancin Albashi

Majalisar tarayya ta tabbatar da dubu 30 mafi karancin Albashi

Majalisar wakilai ta tabbatar da Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin Albashi a kasarnan, majalisar ta tabbatar da hakanne a zaman da ta yi na yau, Talata inda hakan ya saba da dubu 27 da majalisar koli ta aminta dashi.



Zaman majalisar wanda kakakin majalisar, Yakubu Dogara ya jagoranta, ya bayyana cewa sun amincene da rahoton wani kwamiti da suka kafa akan mafi karancin Albashin sannan sun yi la'a kari da irin halin matsin da ake ciki a kasarnan wajan daukar wannan mataki.

Yanzu dai za'a mikawa majalisar dattijai wannan kudiri dan ta tabbatar dashi, a cikin kudirin me kamfani ko wata ma'aikata da yawan ma'aikatan da yake biya albashi basu kai mutum 25 ba baya cikin wannan tsari na biyan mafi karancin Albashi.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post