Karanta amsar da Nafisa Abdullahi ta baiwa wani da yace mata kwalliya ba miji aikin banza
Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta saka wannan kayataccen
hoton nata a dantalinta na sada zunmunta inda masoyanta da dama suka
yaba, saidai wani ya ce mata, Kwalliya ba miji aikin banza.
Nafisar dai ta bashi amsar cewa, Kaina na yiwa.