Kannywood Atiku zata zaba>>Yakubu Muhammad

Kannywood Atiku zata zaba>>Yakubu Muhammad

Taurarron fina-finan Hausa, Yakubu Muhammad ya bayyana cewa, masana'antar Kannywood dan takarar shugaba kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar zata zaba saboda suna fatan zai tallafa musu idan ya zama shugaban kasa.



Yakubu Muhammad ya bayyana hakane a wajan wani taro na musamman da wakilan Atiku Abubakar suka yi na jin ra'ayin jama'a a Kaduna, kamar yanda Punch ta ruwaito.

Yakubu yace suna yin fina-finai marasa inganci wanda matsalar rashin shugabanci na gari ne ya jawo hakan.

Sannan a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zai iya tuna cewa, ya bayar da tallafin miliyan 200 ga masana'antun nishadantarwa. Dan haka Atiku zasu yi.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post