Atiku ya shiga kasar Amurka

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar kenan a wadannan hotunan bisa rakiyar kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki inda ya isa kasar Amurka a yau, Alhamis.



Atiku ya bayyana ta shafinshi na dandalin sada zumunta cewa ya isa babban birnin kasar Amurka, Washington D.C inda zai gana da wasu jami'an gwamnati da 'yan Najeriya mazauna kasar ta Amurka da kuma wasu 'yan kasuwa.

An dai jima ana zargin cewa Atikun ya ki zuwa kasar Amurka saboda zargin shi da rashawa da ake kuma da zarar ya shiga za'a kamashi.



Post a Comment (0)
Previous Post Next Post