Duk wanda ya dawo APC an yafe mai zunubansa>>Adams Oshiomhole

Duk wanda ya dawo APC an yafe mai zunubansa>>Adams Oshiomhole

Jam'iyyar APC ta bayyana cewa duk wani dan siyasar da ya shigo cikinta daga wata jam'iyyar to duk wani laifin da yayi a baya ya sha lallai domin kuwa an yafe masa.



Shugaban jam'iyyar Adams Oshiomhole ne ya bayyana haka a gurin taron yakin neman zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya faru yau a Benin inda jam'iyyar ta karbi wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP da suka koma APC a jihar.

Yace duk wanda ya dawo APC ya kwantar da hankalinshi dan an yafemai zunubanshi.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post