Abokaina zan azurta ba iyalina ba ida naci zabe>>Atiku

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya tabbatar da cewa zai azurta abokanshi idan ya ci zabe, Atikun ya bayyana hakane a wajan wata ganawa da yayi da jama'ar jihar Legas a taron da yayi dasu akan kasuwanci.



Channels ta ruwaito Atiku na cewa idan aka zabeni Abokaina zan azurta ba iyalina ba.

Ya kara da cewa akwai matsalane a cikin azurta abokaina da zan yi? Matukar dai babu rashawa da cin hanci a cikin harkar to babu matsala a cikin azurta abokan na sa da zai yi.

Atiku ya kuma jaddada cewa zai sayar da kanfanin mai na kasa, NNPC idan ya ci zabe.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post