‘Yan sanda 167 da ake nema bayan sun tsere saboda tsoron tunkarar Boko Haram

‘Yan sanda 167 da ake nema bayan sun tsere saboda tsoron tunkarar Boko Haram

A wani labari mai nuna samun cikas da koma-baya wajen yaki da ta’addanci, wasu jami’an ‘yan sanda 167 sun tsere da wurin yi musu horon atisaye, bayan sun ji cewa idan sun kammala, za a tura su ne Arewa maso Gabas, domin su yi yaki da Boko Haram.


Wadannan ‘yan sanda wadanda aka yi kururuwar neman su ruwa a jallo, za su fuskanci hukunci mai tsanani idan aka kama su.

Su na cikin jami’an ‘yan sanda 2,000 wadanda Sufeto Janar ya tsamo, domin kai daukin taimaka wa sojoji wajen yaki da ta’addanci.

An kuma tabbatar da cewa a lokacin da suka arce, babu daya daga cikin su wanda ya damka bindigar da ke hannun sa ko harsasai.

Wanda hakan kamar yadda PREMIUM TIMES ta kalato, wata babbar bazarana cewa matuka.

An dai tura su ne a Makarantar Horas da ‘Yan Sanda ta Musamman da kwe Buni Yadi, Jihar Yobe.

Sai dai kuma a lokacin da suka samu labarin cewa za a tura su ne domin su yi yaki da Boko Haram, musamman a kan iyakar Najeriya da Nijar da kuma Kamaru, sai suka fara sulalewa su na gudu tun cikin makon da ya gabata.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan sandan na Mobile na tunanin fadawa cikin irin halin da wasu sojoji suka rika shiga inda wasu manyan jami’an su ke yin kashin-dankalin da aka karshe su kananan jami’an da ak e turawa ne sa kan rasa raukan su a hannun Boko Haram.

GA CIKAKKAKEN SUNAYEN SU NAN A KASA:




Post a Comment (0)
Previous Post Next Post