Wasu daga cikin ‘yan asalin kasar Wurno dake jihar Sokoto sun karyata
maganar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na cewa da yayi
wai iyayen sa na da asali daga kasar Wurno.
Shugaban kungiyar manoma Tafarnuwa, da shinkafa na karamar hukumar Wurno
Murtala Wurno da Kabiru Wurno sun karyata wannan zance inda suka kara
da cewa Atiku yayi haka don neman yabo da siyasa kawai.
” A Kasar Wurno ne aka haifi sarkin musulmi na farko wato dan marigayi
Usman Danfodio, Muhammadu Bello. Bai kamata Atiku ya shirga wa ‘yan
Najeriya irin wannan karya ba da rana tsaka wai shi dan wannan yanki ne.
” Muna kira ga Atiku da ya maida hankalin sa wajen fadin gaskiya da
tarerayar mutane a siyasar sa ba wai shirga karya ba don neman jama’a.
Idan ba a manta ba Atiku ya shela wa taron ‘yan jam’iyyar PDP a garin Sokoto cewa iyayen sa ‘yan asalalin kasar Wurno ne.
Premiumtimeshausa.