Kiwon Lafiya Amfanin Lemongrass A Jikin Dan’Adam



Ciyawa-mai-kamshin-lemu shuka ce mai dadin kamshi, wato wata irin ciyawa ce doguwa mai launin kore da kamshin lemun-zaki.

Duk da yake dai ba ta da alaka da lemun-zaki, kamshin ciyawar mai karfi da dandano ya yi kama dana lemun-zaki, amma ba ta da zaki.

Ana samun ciyawar a kasashe masu yanayin zafi ko yanayin dumi.

Anfi yawan amfani da ita a kasashen Asiya, Afirika da kuma Australia .

Haka kuma anfi yawan amfani da wannan ciyawa a kasashen Asiya wajen girki.

A kasar Indiya kuwa akan yi amfani da ita a matsayin maganin gargajiya.

Ana amfani da
busassar ciyawar ko danyar ta domin amfani na daban-daban.

Kuma anfi amfani da ita wajen hada shayi , miya ko kori domin ta zamo hadin kayan kamshin girki.

Ana samun manta a kasuwa wanda shima ake amfani dashi.

Mai yiwuwa ne kana da wannan shuka a gida ko a lambunka , koma kana amfani da ita, to amma baka san ainahin amfaninta taba ga lafiya, kawai dai ka dauke ta shuka ce domin kawata gida ko filebo mai sa kamshi a kofin shayinka a lokacin da kake kurbawa.

To ka bude idanunka, domin kuwa wannan ciyawa amfanin ta ya wuce na adon gida kadai ko kamshin shayinka da kake jin dadin sha saboda dandano da kamshin da take baka a lokacin da ka yi amfani da ita.

Ciyawar Lemongrass nada ado da za ta iya yima lafiyar ka domin inganta ta.

1. Kariya Daga Ciwon-Daji/Kansa Shukar lemongrass nada sinadari mai kamshi na “citral”, wanda binciken kimiyya ya nuna cewa yana kashe kwayoyin halitta da ciwon kansa ya harba a jiki. Haka kuma yana inganta lafiyar kwayoyin halittar jiki gaba daya.

2. Karin Jini Da Hana Rashin Jini:Lemongrass nada sinadarin “iron” mai yawa, wato sinadari maisa karin jini domin cikakkiyar lafiya da kuma hana wasu matsalolin rashin jini.

3 Rage Hawan Jini :Yawan sinadarin “potessium” a cikin lemongrass, sinadarin mai inganta lafiyar zuciya, koda da sauran sassan jiki, na taimakawa wajen hana hawan jini, cututtukan zuciya, mutuwar sashen jiki, ciwo kansa, matsalolin rashin narkewar abinci da rashin haihuwa, cikin yardar Allah.

4. Kariya Da Hana Girman Kananan Halittu masu haddasa cututtuka a jiki da kuma hana kumburi, wuri, yayi ja, da radadin ciwo a jiki, musamman taimako ce ga masu ciwon gabbobi da sassan jiki da sauransu.

5. Yaki da cututtukan bakteriya dana fangas: Don haka tana maganin zazzabin cizon sauro da taifot idan an yi shayi da ita, da sauransu. Haka kuma tana maganin cin ruwa na yatsun kafa da makero idan an yi amfani da manta dai da sauransu.

6. Maganin Mura, Zubar Hanci Da Hawaye, Kaikayin Ido, Atishawa, Toshewar Hanci

7. Tace duk wani abu mai guba ga jiki Musamman na abinci, ko wani abu mai cutarwa da fitar da su daga jiki. Tana tsaftace hanta, koda, mafitsara da sauransu.

8. Inganta Bacci Da Kuma Yakar Rashin Bacci: Lemongrass nada tasiri wajen kwantar da hankali da fada da rashin bacci domin samun cikakkiyar lafiya.

9. Taimako Ga Masu Ciwon Suga: Tana rage yawan suga cikin jini, tsarkake saifa da inganta aikinta.

10. Inganta Kwakwalwa: Lemongrass na taimakawa kwakwalwa wajen maida hankali don lakantar karatu, rike karatun da kuma taimakawa wajen sarrafa karatun dama ilimi. Sinadarin “magnesium”, “phosphorus” da “folate” da ake samu a cikin ciyawar nada tasirin kyautata lafiyar kwakwalwa.

Daga leadership


Post a Comment (0)
Previous Post Next Post