An kori Shugaban qungiyar, Haruna Aliyu Ningi
Abubakar Sani zai maka qungiyar a kotu
A yanzu dai rikicin da ya kunno kai cikin qungiyar mawaqan jam’iyyar APC ta arewacin qasar nan da aka fi sani da ANMFO ya dauki sabon salo, inda a yanzu kwamitin majalisar qoli na qungiyar ya kori shugaban qungiyar, Haruna Aliyu Ningi.
Idan ba a manta ba shi Haruna Aliyu Ningi da kuma mawaqi Abubakar Sani ne suka tattauna da jaridar Rariya inda suka yi zargin cewa, fitaccen mawaqin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya yi sama da fadi da kudin qungiyar mawaqan Arewa na jam’iyyar APC (ANMFO) har kimanin Naira miliyan 100 da Qungiyar Gwamnonin Arewa ta ba mawaqan qungiyar a kwanakin baya.
Jaridar ta rawaito cewa mawaqi, Abubakar Sani ya ce kusan mawaqa 500 da suka bada gudummawa wajen nasarar gwamnatin APC, to wadanda suke amfana da gwamnatin ba su fi mutum biyu zuwa uku ba.
Jaridar ta ce, Abubakar Sani ya ce, “Idan ka duba da yawa daga cikin mawaqan da aka yi waqar ‘Lema Ta Yage’ da su, duk sun dawo daga rakiyar Rarara saboda yadda yake amfani da sunansu yana bin manyan jiga-jigan APC yana karbar kudi.”
Abubakar Sani ya qara da cewa wani kuskure da aka samu kan badaqalar kudin shi ne, rashin samar wa qungiyar asusun ajiya, inda Rarara ya riqa amfani da asusun ajiyarsa wajen ajiye kudin.
Shugaban qungiyar mawaqan kafin majalisar ta yi iqrarin korar sa daga qungiyar, Haruna Aliyu Ningi da ke Jihar Bauchi, ya bayyana wa Rariya cewa, Gwamnan Jihar Zamfara ne ya ba su kudin bayan sun buqaci hakan sakamakon irin gudunmuwar da suka bayar a yayin zabukan 2015.
Jaridar ta rawaito cewa Ningi ya ce, tun da farko Rarara ne ya shige gaba wajen karbo kudaden kuma, “ya tabbatar mun da cewar Gwamnan Jihar Zamfara AbdulAziz Yari ya fara bayar da Naira miliyan 60, sai dai wadanda suka yi hanya har aka bayar da kudaden ya ba su Naira miliyan 18.”
Sai dai a yayin zaman kwamitin majalisar qolin qungiyar wanda aka yi a Kano a ranar Asabar din da ta gabata, majalisar ta yanke hukuncin korar shugaban qungiyar Haruna Aliyu Ningi bisa zargin da suka yi cewa ya canza sheqa zuwa jam’iyyar NNPP.
Wata majiya ta tabbatar wa Aminiya cewa a yayin zaman kwamitin akwai Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, Isma’il Na’Abba Afakallah da jarumi Nura Hussaini da sauransu, inda kuma kwamitin nasu ya kuma kori Ibrahim Yala sakamakon zama ummul’aba’isin kitsa duk fitunun da suke damun qungiyar.
A takardar bayan taron da majalisar qungiyar ta fitar a ranar 2ga Yuni, 2018 wanda Alhaji Garba Gashwa ya sa mata hannu, ta bayyana cewa sakamakon zama da Kwamiti na Koli (Board of Trustee) na qungiyar ANMFO ya yi a kan matsalolin da suke damun wannan qungiya ta ANMFO ne, sai majalisar qoli ta dattawa ta samar wa qungiyar matsaya uku.
Takardar ta qara cewa matsaya ta farko ta qunshi korar shugaban qungiyar na qasa, Haruna Aliyu Ningi sakamakon ficewarsa daga jam’iyyar APC ya koma mai Kwando wato NNPP mai kayan dadi.
“Kuma har ya yanki katin jam’iyyar zai yi mata takarar dan majalisar qasa, kuma har ya yi waqoqi na batanci ga ’yan wannan jam’iyya tamu ta APC. Sharadin zama a qungiyar ANMFO shi ne ka zama dan jam’iyyar APC, kuma ka kare mutuncin gwamnoninta da yada muradun shugaban qasa Muhammadu Buhari, wannan dalili ya sa Ningi muka sallame shi.” Inji majalisar.
Majalisar ta qara da cewa matsaya ta biyu da ta cimma ita ce, yanke hukuncin korar mambanta Ibrahim Yala saboda duk fitunun da suke damun qungiyar to shi ne ya qulla su, sannan ya ci gaba da yada su a kafar sada zumunta ba tare da yana da hujja ko makama ba.
Majalisar ta ce, “Sannan (Yala) ya yi qoqarin bata wa shugaban dattawa na wannan qungiya suna da hada fitina tsakanin ’yan qungiya don biyan buqatar kansa da ci wa masu taimaka wa wannan qungiya mutunci da kuma yi musu sharri don bata musu suna. Wannan dalili ya sa muka kore shi.”
Majalisar ta kuma bayyana cewa ta dakatar da mambar qungiyar na Kano, Jamilu Jadda Garko da Ma’aji na qasa na qungiyar, Isyaku Muhammad Forest da Shugaban qungiyar na Abuja, Ahmad Kaka da Shugaban qungiyar na Kano, Jamilu Darmanawa da kuma mamban qungiyar ta Jihar Yobe, Jamilu Roja.
Majalisar ta bayyana cewa an dakatar da su ne bisa wadansu dalilai, inda da zarar an kammala bincike za a sanar da sauran mambobin qungiyar.
Majalisar ta kuma sanar da cewa mawaqi Abubakar Sani da yake ta batatu a kan batun ma ba dan qungiyarsu ba ne.
A lokacin da Aminiya ta tuntubi daya daga cikin wadanda aka kora Ibrahim Yala don jin ta bakinsa, sai ta samu lambobinsa ba sa tafiya, inda bayan Aminiya ta gudanar da bincike ne ta tabbatar da cewa Yala yana qasar Saudiyya don gudanar da Ummara.
Aminiya ta tuntubi Al-Ameen Afandaj wanda shi ne Manaja kuma mai magana da yawun fitaccen mawaqi Dauda Kahutu Rarara kan batun lokacin da mawaqin zai kira taron ’yan jarida don ya yi bayani kan zargin da ake yi masa na yin sama da fadi da Naira miliyan 100, sai ya bayyana cewa mawaqin yana qasar Saudiyya don yin Ummara.
“Rarara yana Saudiyya don yin ummara, amma da zarar ya dawo to zai kira taron ’yan jarida, kuma kai ma kana cikin wadanda za a kira.” Inji Afandaj.
Aminiya ta tuntubi mawaqi Abubakar inda ya tabbatar da cewa shi ba dan qungiyar ba ne, inda a yanzu ya shirya shi da mabiyansu kimanin 300 don maka qungiyar a kotu.
Ya ce, “Mun kai kimanin 300, kuma na shirya jagorantar mawaqan don maka qungiyar ANMFO a kotu matuqar ba su daina kiran kansu qungiyar mawaqan APC na Arewa ba, qungiyar nan gaba daya watanta takwas, sannan indai maganar wadanda suka yi wa APC wahala ne akwai wadanda suka mutu ma, shi ke nan don sun mutu sai a ce babu hakkinsu a cikin tallafin da aka bayar, ba zai yiwu ba, kamar biyan bashi ne, idan har an bada kudin, to ya kamata a ba kowa.”
Ya qara da cewa “ka tuna tun da aka aka ci zabe ba a yi waqa kamar ‘Lema Ta Yage’ ba, don haka wadanda suke cikin qungiyar da aka yi ‘Lema Ta Yage’ da su ba su wuce daga Rarara sai Alfazazee ba, sai kuma irinsu Umar M Shareef, babu ni, babu Adamu Nagudu da Adam A Zango da Hussaini Danko, shi ke nan an bayar da tallafi kan wadanda suka yi wa jam’iyya hidima a 2015 sai a manta da mu? Don haka ba ta zama qungiyar mawaqan Arewa na APC ba.”
Har yanzu ni ne shugaban qungiya – Ningi
A lokacin da Aminiya ta tuntubi Haruna Aliyu Ningi kuwa sai ya ce takardar korarsa da aka fitar daidai take da wasan kwaikwayo, domin wadanda suka zauna har suka zartar da wannan takarda ba wai ’yan asalin qungiyar ANMFO ba ne, ba kuma dattawan qungiya ba ne.
Ya ce, domin asalin dattawan qungiyar babu wanda bai yi magana da shi, kama daga Ibrahim dan dagwas da Shu’aibu dan Midi da Garba Gashuwa, kuma sun ce ba su san komai dangane da takardar ba.
Ya ce, a takardar sun sa sunan shugaban majalisar qoli na qungiyar amma ba shi ya sa hannu ba.
“Abin da ya faru shi ne, an ma tashi daga zama cewa za a kafa kwamiti na mutum biyar don ya duba rikicin qungiyar, an sa ’yan kwamitin su yi bincike, inda kafin wani abu shi aka fitar da wannan sanarwar kora da kuma dakatarwar, an ce za a tattauna komai zuwa bayan Sallah, amma wadansu suka je suka yi gaban kansu, ka ga ya zama wasan yara,” inji shi.
Da Aminiya ta tambaye shi cewa a takardar an yi zargin ya koma jam’iyyar NNPP shi ya sa aka kore shi daga qungiyar, sai ya ce,
“ita ANMFO ba a kafa ta a kan jam’iyyar APC ba ne, an kafa ta ne a kan maganar Buhari ne kawai, ko kana APC ma idan ba ka Buhari to ba za ka shiga cikinta ba, akwai mawaqa ’yan APC ne, amma an qi a sa su saboda ba sa ra’ayin Buhari, irinsu Abubakar Sani da Naburuska da suke Kwankwansiyya an qi tafiya da su, don haka ko ba ka APC idan kana tafiyar Buhari to ka cancanta ka shiga ANMFO.”
Ya jaddada cewa don haka har yanzu yana nan a kan shugabancin qungiya, kuma babu wanda ya sauke shi.
Naira miliyan 20 muka ba qungiyar – Gwamnatin Zamfara
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bakin mai taimaka wa Gwamna Abdul’Aziz na Jihar Zamfara, Ibrahim Dosara ya ce gwamnati ba ta da masaniya dangane da batun Naira miliyan 100 da ake zargi an ba qungiyar mawaqan.
Ya ce, gwamnatin Jihar Zamfara ta ba qungiyar mawaqan gudunmuwar Naira miliyan 20 ne a lokacin da shugabannin qungiyar mawaqan suka gana da Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’Aziz Yari a kwanakin baya.
Ya qara da cewa gwamnan ya ba da kudin ne bayan mawaqan sun buqaci ya ba su gudunmuwarsa don su bude ofis a Kaduna, sannan kuma su sayi mota.
Dosara ya qara da cewa a yanzu Gwamna Yari ya tafi qasar Saudiyya don yin ummara, don haka batun ko qungiyar gwamnoni ta ba mawaqa miliyan 100 ta hannunsa, to sai ya dawo za a ji bayani.
Daga: Aminiya