Ganawar da jaruman masana'antar Kannywood suka yi da shugaban majalisar dattijan Najeriya Sanata Bukola Saraki da jarumi Ali Nuhu ya jagoranta tare da wasu taurarin fina-finan Hausa ta jawo cece-kuce tsakanin wasu manyan jaruman masana'antar.
Kamar dai yadda muka samu, wasu jaruman na ganin an saka siyasa tsagwaron ta musamman ma ganin cewa wadanda suka wakilci masana'antar musamman ma ta bangaren mata ba wasu fitattun jarumai bane da aka sani.
Majiyarmu ta samu cewa daga cikin wadanda suka nuna rashin jin dadin su game da hakan hadda Rahama Sadau da kuma Nafisa Abdullahi.
Ita dai Rahama Sadau ta yi magana me kama da shagube a dandalinta na sada zumunta na Tuwita inda ta bayyana cewa, shugaban majalisar tarayya, Bukola Sataki ya gana da sarkin mu da kuma wasu 'fitattu' daga masana'antar Kannywood a bangaren mata dake jan ragamar masana'antar fina-finan Hausa.
Nafisa Abdullahi ta mayar da martani akan wannan batun inda tace ita ba tasan wadannan matan ba ma amma gasu nan da su aka je.
Jarumar, Nafisa ta kara da cewa, babu ta yanda za'ayin masana'antar ta cigaba idan babu hadin kai da gaskiya a tsakanin su, wannan abin kunyane.
Daga nan ne sai Rahama ta kara da cewa, "a gaskiya nayi tsammanin ganin Jamila, Nafisa, A'isha ko Hadiza a cikin wannan tawagar, amma ni dake mun san yanda masana'antar ke gudana, watakila kamun kafarsune yasa akaje dasu, kinga kuwa dole su wakilcemu."
Daga: Naij Hausa