Ali Nuhu da Adam A. Zango basu dogara da Allah ba - Inji Nura M. Inuwa

Fitaccen Mawaki Nura M. Inuwa ya bayyana cewa Ali Nuhu da Adam A. Zango ba su dogara da Allah ba, sannan kuma suna wasa da nauyin da Allah ya dora masu.

M Inuwa ya kara da cewa, a duk lokacin da jaruman suka tashi yin rigima ba a iya su ta ke tsayawa ba, sai ta shafi har mabiyan su. Nura dai ya yi wannan tsokacin na sa ne a kan rikicin da ake yi tsakanin Ali Nuhu da Adamu Zango, wanda ku san kowa yanzu ya fahimci cewa jaruman ba su shiri.

A ranar asabar, 16 ga watan maris mawakin ya rubuta masu wata zungureriyar wasika a shafin sa na Instagram. Ga abin da ya rubuta:

Shawara Zuwa ga Adam A Zango da kuma Ali Nuhu, na ga alama kuna wasa da nauyin da Allah ya dora muku na jama'ar da ke karkashin ku.

Sannan kuna kokarin raunana imaninku, domin kuwa alamomi suna nuni da baku dogara da Allah ba! duba da tsoran da ku ke nunawa junanku, sannan duk lokacin da za kuyi rigimar me yasa baku barin ta a junanku sai kun nemo mabiyanku kun jefasu a bala'i, sannan in za ku shirya baku nemansu hakan yana nuni da son kai, da rashin adalci da rashin imani.
fitar ku ku ke dubawa baku duba ta wasu? Wanda suke shiga rigimarku, su sai da rai suna rasa abinci a cikin masana'antar Kannywood dalilin rigimar ku, wanda da ba ku sa su a ciki ba za suyi mu'amala da kowa kuma su nemi halak dinsu.

Amma in kuna rigima wannan ba zai yi aiki da wannan ba, wannan bavzai gaisa da wannan ba, don kawai baku shiri kuna haifar da gaba da tashin hankali da rashin zaman lafiya shi ne soyayyar da ku ke wa kannywood din?

Ko shi ne taimakon na k'asan da ku ke ikirarin kuna yi? ku cire girman kai ku cire rawunan da kuka dorawa kawunan ku na son girma, wane ne sarki, wane ne Yarima, dukanin ku babu wanda aka nadawa wata sarauta duka ku kuka sawa kanku.

In kuma da wanda aka nadawa wani rawani ya fito ya fadawa duniya wuri da kuma lokacin da akayi nadin, babu Sarki sai Allah. Haka kuma babu abin dogaro sai shi daga ALLAH sai Annabi, su ne masu girma kowa a kasa yake ba wanda yafi wani sai wanda yafi tsoran Allah.

Amma kun kasa gane hakan, in kun ga dama ku gyara a zauna lafiya, idan kuma baza ku gyara ba bakin ciki zai sa ku yi tayin baya kuna cutar da kan ku kuma kuna cutar da wasu, karshen mugunta kenan.

Ra'ayi na ba irin na kowa bane, kuma banyi don yabo ko kuma neman wani abu a gun daya daga cikin ku ba, dama bantaba yi ba, kuma Insha Allah ba zanyi ba. don Allah na yi kuma ina so na kasa su daina cutuwa, bana raina yaro kuma bana raina babba, ina son kowa da karuwa ne ba iya kaina ba.

Duk wanda yaji haushi ba zan bashi hakuri ba gaskiya ce, sai na fada komai dacin da za ta yi wa wasu. A karshe ina kira ga duk wanda yasan yana tsoran rasa abinci gun wani kada yayi reposting ni dai babu mai bani sai Allah. Alhamdulillah.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post