Ali Nuhu Ba Ubangida Na Bane Uba Ne - Inji Adam A Zango

Kannywood da wajen ta sun yi zaton cewa, budadiyar wasikar da jarumi Adam A Zangn ya rubuta da irinsu Alh Nuhu yake. Domin ana ganin a kwana kin baya tayi tsami tsakaninsu. Duk da yake sunyi silhu da juna, sanin duk mai hankaline cewa silhu alkairi ne.
Ganin mutane zasu yanke hukunci da igiyar zato, shine dalilin da yasa Adam A Zango ya wallafa wata sanarwa gajeriya a Instangram. Sanarwar dauke take da nuna cewa yanzu tsakanin Adam A Zango da Ali Nuhu da rikici bare kuma gaba.
Ga abinda Adam A Zango ya rubuta a Instangram:
''Ali Nuhu ba Uban gida na ba ne Uba na na ne''.
Inji Adam A Zango.
Wannan ya nunawa duniya cewa, budadiyar wasikar da Adam A Zango ya yi zuwa ga makiyansa to bada Ali Nuhu yake ba. Bisala'akari da abinda yaje a Instangram. Duk wanda ka kira da uba to yana da mahimmanci awajen ka. Dan haka ya zama masoyin ka ba makiyanka ba.
Dan haka Ali Nuhu masoyin Adam A Zango shima A Zango ya yarda da haka.
Daga : Adamu Ciroma
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post