
Jama’a sun fi sanin ta da Washa ko Fati Washa watau sunan Mahaifin ta ya bace.
Jarumar tana lokaci, tana samun aiki fiye da duk wata jaruma domin acikin fim biyar sai ka samu ta fito a uku ko hudu, daga cikin tsoffin finafinanta akwai Sarki, Kadan daga cikin fina-finan wannan Jaruma akwai Ya Allah daga Allah, da tayi a 2014, 'Yar Tasha a 2015 Washa ta fito a Ana Wata ga Wata a shekarar 2015. Sannan ta fito a Mijin Biza, Hindu, Dangin miji, Matar Wani da sauransu.

Fatima ba ruwanta da fada da kowa domin tunda take ba'a taba jinta da wani ko wata ba suna rigima ko kuma jan fada.
Films dinta da zasu fito suna da yawa Irinsu Gamdakatar, Gwaska Returns, Gobarar titi, Rariya, Boyayyen Al'amari da sauransu.
Fati Washa kamar su Rahma Sadau, Hadiza Gabon, da 'Dan wasa Ali Nuhu, dsr tana kan shafin Tuwita na yanar gizo inda ta ke aikawa dinbin masoya da mabiyan ta sako da game da halin rayuwa.