ANA KISHIN-KISHIN SAUKE SHUGABA BUHARI A 2019

- A makon nan ne wata tsohuwar Minista ta kafa #RedCardMovement - Ana yunkurin ba Jam’iyyar APC mai mulki da PDP jan kati ne a 2019 Mun samu labari cewa yanzu haka wasu a cikin Kasar na kutun-kutun din ganin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Jam’iyyar sa ta APC mai mulki sun sha kashi a zabe mai zuwa na shekarar 2019. RedCardMovement ta fara karfi yayin da ake dosar siyasar 2019 Wata tsohuwar Ministar Kasar Misis Oby Ezekwensili ce ta kirkiro wata tafiya da ake kira #RedCardMovement a jiyan nan wanda bisa dukkan alamu za ta fatattaki APC a 2019. Madam Oby tace haka nan kuma ba za su yi PDP ba. KU KARANTA: Jama'a sun yi kasaitaccen biki a Garin Maiduguri Tsohuwar Ministar Obasanjo ta fara hada gayyar kada APC Tsohuwar Ministar Najeriyar tace sun gaji da wannan tafiya ta Gwamnatin APC inda ta nemi Jama’a su mara mata baya su shirya daukar katin zaben su wajen ganin an ba Jam’iyyar APC har ma da Jam’iyyar adawa ta PDP kunya a zaben 2019. Wasu dai na cewa Jam’iyyar APC ta ba Jama’a kunya sai dai kuma da dama a Kasar na ganin PDP ce ta kashe Najeriya. Dalilin haka ne dai tsohuwar Ma’aikaciyar babban bankin Duniyar ta ke ganin dole a tashi a nemi wata mafitar siyasa a 2019.RedCardMovement: An fara yunkurin tika Shugaba Buhari da kasa a 2019
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post