Java Programming A Harshen Hausa Part 2.

java a sauwake 2.
Jiya mun tsaya akan cewa yau zamu tattauna akan yanda mutun zai yi compile na code dinsa,yau insha Allah zamu dora daga inda muka tsaya.
Bismillahirrahmanirrahim.
Burina shine ka fahimci yaren java a tsanake kuma daki-daki,akwaiwasu matakai guda uku da ya wajaba gareka dan hada programm na java.
Dafarko ka tabbata kayi download na application din java,idan baka dashi zaka iya saukar dashi daga babbab shafinsu ko kuma ta wannan link din
www.java.com/ download.
Abun da kake buqata na biyu kuma shine editor(misali:notepad),sai abu na qaeshe da kake buqata shine terminal application.
Manhajojin dazaka iya anfani dasu sune.mac os,windows ko kuma linux.
TSARIN BADA UMURNIN JAVA
masana sun rarraba matakin programming zuwa uku.
1.zaka rubuta umurnin acikin text editor sai kai save dinsa da "myprogram.java"
2.zaka rubuta"javac myprogram" a cikin terminal window danyin compile.
3.zaka rubuta "java myprogram" acikin terminal window danyin running na program dinka.
A matakin farko ka kiriri program,mataki nabiyu ka fassara umurnin zuwa yaren da naura zata iya fahimta wanda a yaren masana kimiyar naura suka kira compile,mataki na uku kuma kayi running na program dinka.
Nanne qarshen darasi na biyu...idan mun kula darasinmu na yau ba programmin bane,matkai ne na rubuta umurni..daga yanzu insha Allah zamu tsunduma programming ne tunda munsan yanda zamui compile na program.
Yaranku Ibrahim Auwal.
Allah yabamu sa'a.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post