Zan So Yarinyata Tayi Harkar Films


Jarumin nan na fina-finan Hausa a
masa'antar Kannywood mai suna Sadiq
Ahmad ya bayyana cewa shi zai so diyar
sa ta yi harkar fim don bai ga wani abu
ba a cikin ta.
Jarumin ya bayyana haka ne a yayin
da yayi wata fira da majiyar mu dake
wallafa mujallar da ta jibanci harkar
fim a watannin baya.
NAIJ.com ta samu cewa jarumin yayi
wannan bayanin ne a lokacin da yake
ansa wata tambaya da aka yi masa
game da ko zai iya barin diyar sa ta
cikin sa tayi harkar fim.
A ansar da jarumin ya bayar kuwa ya
bayyana cewa tabbas zai iya barin ta
domin kwa ba wani abu bane.
"E, zan iya barin ta ta yi. Ai ba wani
abu bane," in ji shi.
Sai dai kuma ya bayyana cewa ba zai
tursasa mata ba wajen cewa dole sai
ta yi fim din ba inda yace duk abun
da take so shine za ta yi.
A cewar sa: " Kasan bahaushe yace ka
haifi mutum, baka haifi halin sa ba; za ta iya yiwuwa na ce tayi amma ita kuma tace burin ta ta zama lauya ko likita, kaga kenan babu yadda zan yi da ita."
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post