Ni Bazawara Ce Mai YaYa Biyu-Fatima Yola


shahararriyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood wadda ta dade tana bayar da gudummuwar ta masana'antar mai suna Fatima Isa Muhammad Yola wadda aka fi sani da Teema Yola ta bayyana cewa tabbas ta taba aure har ma tana da 'ya'ya biyu yanzu haka amma bata so tana yaya ta hakan saboda yanayin sana'a ta.
Jarumar ta bayyana hakan ne a yayin da take yin fira da majiyar mu ta jaridar Blueprint inda take yin karin haske a game da rayuwar ta a baya da kuma yanzu.
HausaTutoblog dai ta samu cewa Teema Yola ta bayyana babban dalilin da yasa bata son tana yayata zawarcin nata shine saboda kada ta kori wasu mazan dake son ta da aure.
Haka zalika jarumar ta bayyana cewa a kowane lokaci idan dai har ta samu namijin da take so zata yi auren ta domin a cewar ta cikar mace kenan a dakin mijin ta.

1 Comments

  1. Taya za'ayi a samu contact nata domin gabatar da kaina a wajenta ko ta nemeni a wann number 08067873989

    ReplyDelete
Post a Comment
Previous Post Next Post