Kungiyar Mata Yan Film Ta Tarwatse


A'AYIN MUJALLAR FIM A MUJALLAR Fim ta watan Satumba, 2017, kun karanta yadda mata ’yan fim da su ka yi aure su ka yi wani k'warya-k'waryan taron sada zumunta a birnin Kano. Akwai k'ungiya wadda su ka kafa a baya wadda manufar ta ta farko ita ce sada zumunta, sai kuma k'udirin taimakon kai da kai ya biyo baya, da sauran su. Duk wanda ya karanta manufofin k'ungiyar, to ya san cewa abu ne mai kyau. Ya yi daidai da hob'b'asan da ake yi a sauran sassa na jama’a, inda wani ko wasu ke tashi tsaye su kafa wata k'ungiya mai zaman kan ta domin su taimaki ’yan’uwan su marasa galihu. A Turance, ana kiran irin wannan k'ungiya Non-Governmental Organisation (NGO), wato k'ungiyar da ba ta gwamnati ba, da nufin cewar ba sai mutum ya dogara da gwamnati ba wajen yi wa al’umma aiki. Mansurah Isah da Wasila Isma’il ne k'ashin bayan kafa wannan k'ungiya ta ’yan fim mata. Da farko, matan aure ne kad'ai a cikin ta, to amma saboda wasu daga cikin su auren su ya mutu daga baya, ta yadda ba za a iya cewa su fita ba, sai k'ungiyar ta had'o har da zawarawa ’yan fim. Sun lura da cewa wasu ba su da halin taimakon kan su idan wata larura ta taso masu, kamar yadda ya faru ga Fati Sulaiman a bara, inda aka tara kud'i domin yi mata aikin cire mahaifa. Su ’yan fim d'in su ne ke had'a kud'i - tare da neman agaji daga wasu ’yan fim d'in, misali maza, da ma mutanen da ba ’yan fim ba - don had'a abin taimakon da ya kamata. Kada mu manta, da man akwai irin wasu k'ungiyoyin agaji wad'anda wad'ansu ’yan fim su ka kafa wad'anda manufar su ta bambanta da wannan. Su, agaji su ke kaiwa ga mutanen da ba ’yan fim ba, kamar majinyata ko fursunoni da sauran su. Misali, Hadiza Gabon, Nafisa Abdullahi, da ita kan ta Mansurah, duk su na da irin wad'annan k'ungiyoyin. To amma a ce k'ungiyar da ta sadaukar da kan ta ga taimakon mata ’yan fim, sai ita wannan mai suna Kannywood Females Foundation. Tunani ne mai kyau wanda ya nuna cewa ciwon ’ya mace na mace ne, kuma tilas ne mata ’yan fim su tashi tsaye su taimaka wa kan su kafin su yi tsammanin taimako daga wajen wani can daban. Kwatsam, sai labari ya b'ulla cewa an samu b'araka a a k'ungiyar, wai su Saima Mohammed Raga sun ware sun kafa wata k'ungiyar, wato Kannywood Celebrities Foundation. Ita ma tasu k'ungiyar manufar ta iri d'aya ce da waccan ta farkon. Ko sunan su ma iri d'aya ne in ban da bambancin kalma d'aya da aka samu. Abin mamaki shi ne ba fad'a aka yi ba da ya janyo wannan a-raba d'in. Saboda haka dai akwai wata manufa a k'asa. Kamar yadda Mansurah ta yi zargi, kila dai an kafa k'ungiyar ne saboda abu biyu: neman shugabanci da kuma hangen samun kud'i. Abin bak'in ciki ne a ce an samu wannan babbar b'araka tun yanzu, a daidai lokacin da ake k'ok'arin gina k'ungiyar. Duk da yake Saima ta ce wai k'ungiyar su ba kishiyar d'ayar ba ce, a gaskiya ba haka ba ne; da gaske kishiya ce. Haka kuma an haifar da matsananciyar gaba a tsakanin ’yan fim mata masu aure da kuma zawarawa. Yanzu an nuna cewa akwai gida biyu masu adawa da juna, maimakon su kasance tsintsiya mad'aurin ki d'aya. Mu na bada shawara ga wad'annan mata da su daure su sake lale, su koma su had'e k'ungiya guda d'aya. A samu maslaha. Rarrabuwar su ba za ta haifar da d'a mai ido ba, sai ma b'acin rai. In da hali, maza shugabanni a harkar fim su shigo ciki domin su ba su shawara. A gano menene dalilin su Saima na warewa, a ba su hak'uri. Idan batun shugabanci ne, a yi zab'e na gaskiya, duk mai son rik'e muk'ami, ta yi takara. Kuma ya kamata su masu aure a cikin su, irin su Maryam Mashahama da su ka shiga cikin rigimar, su kiyaye shiga cikin rud'ani ko wani abu da zai jawo masu surutu a gari. Su tuna cewa a k'ark'ashin mazajen su su ke; shiga hatsaniya ba tasu ba ce. Su yi wa kan su fad'a, su ja girman su.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post