Bani Da Burin Dena Yin Film-Jamila Nagudu


shahararriyar jarumar nan ta fina-finan kannywood a masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood kuma dadaddiyar fuska da ta dade tana taka muhimmiyar rawa watp Jamila Umar Nagudu wadda aka fi sani da Jamila Nagudu ta yi ikirarin cewa ba tada burin dena yin harkar fim a duk 'yan shekarun nan.
Sanannayirar jarumar dai wadda ta shafe akalla shekarun da suka kai goma a harkar ta fim ta kuma bayyana cewa nasarorin da ta samu a masana'antar ba zasu kirgu ba inda kuma ta kara da cewa har yanzu tana da amannar cewa akwai sauran rawar da zata taka a masana'antar.
ArewaNow.com.ng haka zalika ta samu cewa da take karin haske game da rayuwar tata a masana'antar nan gaba ta yi hasashen cewa ita tana da sha'awar ta zama mai bayar da umurni domin hakan ne kaiwa kololuwa a harkar.
Jarumar dai 'yar asalin garin Bauchi ce kamar yadda muka samu sannan ta kuma mika sakon godiyar ta ga dukkan masoyan ta sannan kuma ta bayyana cewa har yanzu ba su gama ganin rawar ta ba.

1 Comments

Post a Comment
Previous Post Next Post