yanxu yanxu buhari ya isa birnin tarayya Abuja bayan hutun salla da yayi a Daura dake katsina.

Yanxu yanxu Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa babban birnin tarayya wato Abuja bayan ya kammala hutun sa na babban Sallah a Daura wato garinsu dake jihar Katsina.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa jirgin shugaban kasar mai lamba NAF-540 ya baro Daura da misalin karfe 10:24 na safiyar yau Laraba, 6 ga watan Satumba.
Shugaban kasar ya dawo Abuja ne tare da uwargidansa her excellency Aisha Muhammadu Buhari,inda suka samu rakiyan mutane masu yawa.
Ga hotunan nan kusha kallo:


Post a Comment (0)
Previous Post Next Post