ina masu layin glo? ku matso kuci banzaaa


- wowww.Masu amfani da layin nan na Globacom za su samu garabasa ta bowsing.
- Kamfanin GLO ya sanar cewa a wannan makon za a hau yanar gizo kyauta.
- A can kwanakin baya dai an yi kokarin bada wannan garabasa
Yanzu haka labari ya zo mana cewa masu amfani da layin nan na Glo za su samu garabasa ta musamman a karshen makon nan.
GLO tace masu aiki da layin za su gwangwaje kyauta a Ranar Alhamis muddin mutum ya sa katin waya na N250 ko kuma ya sa katin waya N150 kana ya kashe akalla N100 wajen sayen data na hawa shafin gizo a makon yau.
Kamfanin za ta bada wannan garabasa ne dai jibi watau 28 ga Watan Satumban nan inda jama’a za su more a bagas. GLO za ta ba da kyautar mega byte 200 kyauta domin a gwangwaje ayi abin da aka ga dama.
Kwanaki dai Hukumar NCC da ke kula da harkokin sadarwa na zamani ta hana kamfanin bada irin wannan garabasa lokacin da tayi niyya irin haka.
Mu dai munaso ba ruwanmu da wani NNC.
ALLAH YAKAIMU LAFIYA.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post