Waye ya fi amfana da dage zaben 2019? Atiku Ko Buhari

Adhoc ObserversHakkin mallakar hotoAFP
Najeriya za ta gudanar da babban zabenta a ranar Asabar bayan dage zaben da aka yi lokacin wani taron manema labarai da shugaban hukumar ya jagoranta.
Dage zaben kwatsam a dare daya ya bai wa 'yan kasar mamaki kuma hakan ya kawo takura ga dubban 'yan Najeriyar musamman wadanda suka sha doguwar tafiya domin kada kuri'arsu.
Cibiyar masana'antu da kasuwanci ta Legas ta ce hakan ya jawo asarar dalar Amurka biliyan 1 da dubu dari biyar.
Hukumar zaben kasar ta kawo dalilai da dama da suka yi sanadiyyar dage zaben wadanda suka hada da zargin makarkashiya da aka yi musamman ta bangaren jigilar kayyayakin zaben da kuma matsalar yanayi da ya hana jirgin sama tashi domin kai takardun zabe.Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriyar da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP duk sun nuna rashin jin dadinsu dangane da dage zaben kuma jam'iyyun sun zargin junansu da kokarin tafka magudin zabe.

Akwai jam'iyyar da dage zaben zai fi zama alheri a gareta?

A sanarwar da aka fitar ranar dage zaben, jam'iyyar APC ta zargi PDP da kokarin dakushe kwarjinin dan takararta Muhammadu Buhari.
A dayan bangaren jam'iyyar PDP wacce dan takararta shi ne Atiku Abubakar ta zargi cewa hukumar zaben ta jinkirta zaben ne domin bayar da dama domin tafka magudin zabe.
Wata mai fashin baki a kan al'amuran yau da kullum Idayat Hassan da ke cibiyar dimokradiyya da ci gaba a Abuja ta bayyana cewa jinkirta zaben da mako guda ba zai yi wani tasiri wajen gudanar da magudin zabe.
President Muhammadu Buhari and Atiku AbubakarHakkin mallakar hotoREUTERS
Ta kwatanta dage zaben da aka yi a yanzu da kuma na 2015 a lokacin mulkin PDP inda suka dage zaben da kusan mako shida saboda zargin da suke yi na hare-haren Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.
Wancan dage zaben ta bayyana cewa ya zama alheri ga APC inda hakan ya jawo wa PDP bakin jini a matsayin jam'iyyar da ke neman mulki ko ta wane hali.
Amma ta nuna cewa dagen zaben zai iya zama alheri ga APC ma a wannan lokaci saboda za a iya samun karancin fitowar mutane, amma za a iya samun fitowar mutane da dama a wuraren da tun asali ana samun tururuwar fitowar mutane a ranar zabe,
Misali yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas kuma nan ne Buhari ya fi yawan magoya baya.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post