Obasanjo ne jagoran tafka magudin zabe — Bola Tinubu

Bola TinubuHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionBola Ahmed Tinubu ya mulki Legas tsakanin 1999-2007
Uban jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas Bola Ahmad Tinubu, ya gargadi 'yan Najeriya a kan zaben dan takarar shugabanci kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.
A wani taron gangamin yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari a birnin Lagos, Bola Tinubu cikin habaici ya yi tonon silili a kan tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar.
Bola Tinubu, ya ce yana shawartar 'yan Najeriya da su yi hattara kar su yi zaben tumin-dareYa ce ''Zan koya wa Atiku darasi, shi kuwa Obasanjo da ya ke cewa za mu yi magudi, idan za mu tuna a shekara ta 2003 gwamnatin Obasanjo ce ta kawo 'Yar'adua a matsayin shugaba amma shi 'Yar'adua da kansa a cikin jawabansa ya sanar da cewa an tafka mugudi a zaben da ya kai shi ga zama shugaban kasa, don haka Obasanjo ne uban tafka magudi''.
A kan kungiyoyin sa ido na kasashen waje da suke ta kira a kan ka da APC ta ce za ta haifar da cikas ga zaben shugaban kasa, sai ya kada baki ya ce ''Muna marhaban da ku, ku zo ku yi aikinku, ku har hada rahotanninku ku koma kasar ku wannan demokuradiyar mu ce.
Gangamin yakin neman zaben da shugaba Muhammadu Buhari ya yi a Legas, ya tabo batutuwa daban-daban da kuma aniyar shugaban ta ci gaba da yaki da rashawa da inganta tattalin arziki da tsaro a kasar.
Ana sa tsokacin gwamnan jihar Legas Akinwumi Ambode, ya ce wannan zabe ba batu ne na kabilanci ko addini ba, ya shafi zaben dan takara domin samar da ababen more rayuwa don haka a zabi jam'iyyar APC.
Shugaba Muhammadu Buhari dai na neman wa'adin shugabanci Najeriya ne a karo na biyu karkashin jam'iyyar APC.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post