Mun yafe wa Buhari zuwa Zamfara>>Marafa

Daya daga cikin masu neman takarar kujerar gwamnan jihar Zamfara a jam'iyyar APC, wanda bangarensa ba ya ga-maciji da gwamnatin jihar, sanata Kabiru Garba Marafa, ya ce sun dauke wa shugaba Muhammadu Buhari zuwa jihar yakin neman zabe.


A cikin wata hira da ya yi da BBC, sanata Marafa, ya ce jihar Zamfara ta shugaba Buhari ce, kuma su mutanensa ne suna kuma tare da shi tsakani da Allah.

Amma bisa la'akari da abin da ke faruwa a jihar, sanata Marafa ya ce ' Ina son zan ba wa Baba shawara na cewa mun dauke masa zuwa jihar Zamfara, ya bari mu za muyi masa duk abin da ake yi, kuma kuri'unsa ba bu abin da zai taba su'.

Ya ci gaba da cewa 'Amma idan mai girma shugaban kasa ya ga cewa yana so ya je Zamfara, to za mu roke shi ya sawwake mana zuwa tarbarsa a ranar da zai zo, idan dai har gwamnatin jihar za ta tarbe shi'.




Sanata Marafa, ya ce, idan har shugaban kasar ya je jihar, to bayan ya tafi su za su hada masa gangami in ya so sai ya tura wakili ya gani, sannan kuma za su sa a haska gangamin a gidan talbijin na kasa NTA.

Wadannan kalamai na sanatan, sun zo ne bayan ikirarin da ya yi cewa suna da kwarin gwiwa za su shiga zabuka duk da matsayar hukumar zabe.

Hukumar zabe ta kasa dai ta sake jadada matsayarta cewa jam'iyyar ta APC ba ta da 'yan takara a jihar Zamfara saboda rikicin da ya faru a lokacin zabukan fidda gwani.

Jam'iyyar APC a jihar dai ta rabu gida biyu, wato akwai bangaren gwamnan jihar mai ci Abdul'aziz Yari da kuma daya bangaren.

Rikicin siyasa a Zamfara dai ya samo asali ne bayan da Gwamna Abdulaziz Yari ya sanar da goyon bayansa ga kwamishinansa na kudi, Alhaji Muktar Shehu Idris, a matsayin wanda zai gaje shi.

Wannan ne ya sa wasu daga cikin masu sha'awar takarar gwamnan a jam'iyyar APC su takwas da suka hada da mataimakin gwamnan Ibrahim Wakalla da kuma Ministan tsaro Mansur Dan Ali suka hade kai domin yakar gwamnan na Zamfara.

Sau biyu ana shirya zaben fitar da gwanin a jihar, amma sai a soke shi saboda rikicin siyasa tsakanin bangarorin jam'iyyar a jihar.

Jam'iyyar APC a jihar ta Zamfara bangaren gwamnan jihar, ta ce sakamakon wani hukuncin babbar kotun jihar a Gusau, a ranar Alhamis, ta mika wa hukumar zaben ta tarayya jerin sunayen 'yan takararta a zabukan da za a yi batun da hukumar zabe ta yi watsi da shi.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post