Sakonni zamu turawa mutane: Bazan yi amfani da kudin gwamnati wajan yakin neman zabe ba>>Buhari

Sakonni zamu turawa mutane: Bazan yi amfani da kudin gwamnati wajan yakin neman zabe ba>>Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai taba bari a taba asusun gwamnati ba dan daukar kudi a mishi yakin neman zabe ba.



Buhari ya bayyana hakane ta hannun me magana da yawunshi, Malam Garba Shehu bayan  kammala taron majalisar koli jiya, Laraba.
Ya bayyana cewa a yi amfani da sakon wayar hannu da sauran kafafen sada zumunta dan neman kuri'un 'yan Najeriya, ni bazan fitar da kudi dan a baiwa mutane su zabemu ba, injishi.
Yace 'yan Najeriya na bukatar canji, dan haka an daina siyasar bayar da kudi ga masu zabe dan su zabi dan takara.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post