Man City ta fi kowa cin kwallaye a Turai



Manchester City ta zama ta farko da ta zura kwallo sama da 100 a tsakanin manyan kungiyoyin da ke buga gasar Lik-Lik ta Turai ta kakar 2018/19.


A ranar Lahadi City ta ci Huddersfield 3-0 a wasan mako na 23 a gasar Premier, kuma Danilo ne ya fara cin kwallo, wadda ita ce ta 100 da ta zura a raga a dukkan fafatawa da ta yi a bana.

Daga baya ne ta kara biyu a karawar ta hannun Raheem Sterling da kuma wadda Leroy Sane ya ci, jumulla City tana da kwallo 102 da ta zura a raga a wasannin da ake yi.

'Yan wasa 17 ne suka ci wa City kwallo 102 a kakar bana, inda Sergio Aguero da Gabriel Jesus kowanne ya ci 14, sai Sterling mai 12 da kuma Sane wanda ya ci 11.

Tun bayan da Crystal Palace da Leicester City suka yi nasara a kan City a Premier, kawo yanzu ta dura kwallo 22 a raga a wasa hudu da ta buga.

A kakar 2013/14 City ta lashe kofin Premier ta kuma zura kwallo 156 a karkashin jagorancin Manuel Pellegrini a dukkan gumurzun da ta yi a kakar.

Paris Saint-Germain ce ke biye da City a yawan cin kwallaye a bana, bayan da ta zura 90 a raga, sai Barcelona ta uku mai guda 78.
BBChausa.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post