Ko a dajin Sambisa za'a ajiye akwatin zabe zamu je mu sakawa Buhari kuri'a>>Inji wani dan jihar Yobe

Ko a dajin Sambisa za'a ajiye akwatin zabe zamu je mu sakawa Buhari kuri'a>>Inji wani dan jihar Yobe

Wannan wani hoton masoyan shugaban kasa, Muhammadu Buharine a jihar Yobe inda yaje yakin neman zabe, jiya, hoton ya dauki hankula saboda irin sakonnin da mutanen ke dauke dashi a kan kwalayen da suke rike dasu.



Daya daga cikin kwalayen yace, na yadda da Buhari fiye da yadda na yarda da kaina.

Dayan kuwa yace, mu 'yan jihar Yobe dole mu sake zabenka a karo na biyu ko da kuwa a dajin Sambisa za'a ajiye akwatin zaben.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post