Zamu iya yin ko menene dan a hadamu da Ali Nuhu>>Inji wasu mata



Me gudanar da shafin masoyan tauraron fina-finan Hausa, Ali
Nuhu na dandalin Twitter ya bayyana labarin yanda aka
samar da shafin da kuma magance matsalar cewa Alin yana
da girman kai.
A cikin labarin da ya bayar yace mafiya yawan masu cewa
Alin nada girman kai mata ne saidai Alin na kaffa-kaffa da
sune saboda irin aniyar da wasu daga cikin su ke nufar
jarumai da ita.
Yace, koda shi dake gudanar da wannan shafi yakan samu
sakwanni marasa kan gado da wasu matan ke aikomai inda
sukan ce zasu iyayin koma menene dan a hadasu da Ali
Nuhu.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post