Za'a samu rikici a lokacin zaben Najeriya>>Inji kasar Amurka

Kasar Amurka ta bayyana cewa a babban zaben Najeriya me
zuwa da za'ayi a shekarar 2019 idan Allah ya kaimu za'a
samu rikici.
Me baiwa shugaban kasar Amurkar shawara akan harkokin
kasashen Afrika, Tibor Nagy ne ya bayyana haka a wajan
wani taro da aka yi akan zaben na Najeriya a birnin
Washington DC daya gudana a ranar Alhamis din data
gabata.
Tibor Nagy ya kara da cewa, saidai rikicin da za'a samu ba
na gaba daya kasar bane, za'a samu rikicinne a jihohin Kano,
Rivers, Borno, da Benue.
Yace zaben na shekarar 2019 na da muhimmanci ga
dimokradiyyar Najeriya kuma kasar Amurka bata goyon bayan
ko wane dan takara amma zata saka idanu dan ganin yanda
zaben zai gudana.


Post a Comment (0)
Previous Post Next Post