*Haske writer's Association* (home of expert and perfect
writer's)
*SIRRIN MIJINA*
*Billy Galadanchi*
Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*
*Salon rubutun wannan littafin yasha banban da
wanda na saba rubutawa, zakuci karo da kalmomi masu
nauyi aciki wanda wasu zasu kalla a matsayin
batsa,sedai kuma ba batsar bace haka salon rubutun yake
saqon mu baze isa ba se dole ta wannan hanyar sabida
haka dan Allah kar wacce ta zageni, idan kinji bazaki iya
biba ki hakura da karbar saqon, Allah yaga zuciyata kuma
kowa ya sanni bana wannan shashancin a books nawa
sam.....sabida haka dan Allah banda zagi*
01
Cikeda nutsuwa Nafeesah ke tafiya cikin uniform d'inta
kalan light and dark purpule na makaranta nursery da
primary ta cement primary school dake jihar sokoto a
unguwar Wurno road, sauri take janye da hannun qaninta
shuraim yayanta sudais ya musu nisa acewarsa idan yayi
late shi kadai za'a doka a school, duk yawan horn da ake
rafka musu be saka ta tsaya ba seda tajiyo muryan
qawarta Zuhrah tana kwalla mata kira sannan taja birki ta
tsaya ta waigo tana kallon ta,washe baki zuhra qwasai tai
sannan tace tana mata alama da hannu
"Kizo mana a diremu a school tare munyi late kuma naje
gidanku mami tace kin wuce tuni" murmushi itama
Nafeesah tayi sannan tajuya riqeda hannun qaninta
shuraim suka shiga motar ta kalleta tace
"Aunty qwasai sarakan surutu kinji yanda harshenki ke
tashi kuwa,kinfasan mami tace ba kyau mace magana
tana d'aga murya ke bakya ji" tsaki taja tace
"Sunana Aunty qwasai kuwa fad'i ki qara,nifa Nafee
nafiso ki gano cewar muryana Allah yamun shi a haka
bawai nice nake rakad'i ba,kinga ni bama wannan kinsam
wai jiya daddy ya dawo bari kiji tun daga kan Apple babu
wani nau'in 'ya'yan itacen dabe kawo mana ba,bari ma
kiga yau lunch box dina babu ne kurin babu aciki" inda
sabo Nafeesah ta saba da wannan halin yawan surutun
na qwasai se ttace a qoqarin kawarda zancen
"Kinyi home work da aka bamu na maths kuwa?"
murmushi tayi
"kinsan ni sam bana wasa da home work,tuni nayishi
wollah m" bata qara cewa komai ba har suka isa qwasai
keta faman zuba, kai tsaye class takai shuraim dake
nursery 3 ta wuce parimary 5 dama nanne class d'insu.....
Bayan da aka tashi break ma bakin Aunty qwasai be
mutu ba, duk wani dan ajin dasuke dashiri seda ta bashi
labarin tsarabar da daddy ya kawo musu daya dawo
daga kaduna jiya, Nafeesah se faman hanata takeyi
amma abin yaci tura kowa se kallonta yake tana zuba
"Mommy ma fad'a takeyi da daddynmu wai ze qara aure
tace inka isa,bakiga yanda ta burgeni ba datamai masifan
yanzu ai dolenshi jiya naji yana bata haquri akan ya fasa
qarin auren" wani takai nafeesa taji
"Kekam zuhra wai duk hiran gidanku semunji ne ko waya
tambayeki ne anan wurin?" gwalo ta mata
"Kurun dai kice bakyaso in gaya musu en Nepa sunzo
sun gutsure wutar gidanku tun ranar juma'a,koki rantse
ba'a gidanmu kikai gugan uniform naki ba? Tunda ban
gaya ba aiba ruwanki dana mu gidan" takaici ya ishi
Nafeesah dama gata da qarancin shekaru amma akwai
hankali, batace komai ba tabar wurin yayinda d'aukacin
yaran dake wurin suka kwashe da dariya abin yayiwa
Nafeesah ciwo ya sanya ta fasa yin break gaba d'aya
takoma class ta zauna tana kuka, a haka Nihla tazo ta
sameta ta riqe mata hannu
"Pheey dan Allah idan Aunty qwasai tana sha'aninta kina
zura mata ido,kinsan halin zuhra sarai duk sanda kike
mata gyara lokacin take miki wani tonon sililin ni breakfast
d'inma ki dena zuwa field nima zanna riqa tsayawa anan
munayi a tare" share wayanta tayi abinka da yaro seta
ware suka ci abincinsu a class suna hira, koda aka tashi
jan hannun shuraim tayi suka nufi hanyar gawon nama
inda dama nanne asalin unguwar su suda su Zuhrah
gaba d'aya, can daga mota Aunty qwasai ta kware
muryanta