Dattawan Jihar Kano Sun Bukaci Yan Sanda Su Binciki Gwamna Ganduje

Wasu Dattawa a jihar Kano sun yi kira da babbar murya ga
gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya fito yayi wa mutanan
kano bayani akan faifan bidiyo da ake zargin ya nuna shi
yana karbar cin hanci daga gurin yan kwangila.
Kimanin makonni biyu bayan da babbar kotun Kano ta
haramtawa Majalisar dokokin Jihar bincikar faifen bidiyon
dake zargin gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana karbar cin
hancin dala miliyan biyar, dattawan Kano sunce akwai
bukatar gwamnan ya yiwa al'umar jihar bayani da zai gamsar
da su game da zargin.
Hakan dai na zuwa a dai-dai lokacin da jama'a ke korafi kan
yadda dattawan na Kano suka ki cewa uffan tun bayan da
Jaridar Daily Nigeria ta fara kwarmata zargin karbar rashawar
akan gwamna Ganduje.
Daya daga cikin dattawan Jihar Kano, Alhaji Gidado Mukhtar,
yace abu na farko da ya sa dattawan ba su yi magana ba
shine domin maganar tana gaban kotu, da bisa doka bai
kamata a saurara, na biyu kuma magana irin wannan idan ta
taso ya mata a tsaya a ga inda ta gangara kafin aga mene ne
a ciki.
Gidado yakara da cewa tunda kotu tayi hukunci ‘yan sanda
suna da hakki da kuma damar su bincika wannan zargi da
ake yiwa gwamna Abdullahi Umar Ganduje, yanzu suna
sauraron ‘yan sanda su yi aikin daya kamata wajen bincikar
wannan zargin karbar cin hancin.
VOAhausa.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post