Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar ya bayyana takaicinshi akan irin yanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari ko mataimakinshi babu wanda ya samu halartar jana'izar sojojin da suka rasa rayukansu a harin Metele da aka yi yau, yace wannan abune wanda ba za'a yadda dashi ba.
Atiku ya bayyana cewa, a cikin wata sanarwa da ya fitar da jaridar Thisday ta wallafa, ya ga hotunan jana'izar sojojin da suka rasa rayukansu a yakin da suka yi da Boko Haram a Metele kuma yana mika ta'a ziyyarshi ga dukkan jami'an soji da iyalansu sannan yana fatan Allan ya baiwa iyalan mamatan juriyar rashin da suka yi.
Ya kara da cewa saidai abin takaici shine rashin zuwan shugaba Buhari gurin jana'izar sojojin ko kuma mataimakinshi Osinbajo ko kumama su wakilta wasu jami'an gwamnati su halarci jana'izar dan girmama wadannan sojoji da suka rasa rayukansu.
Atiku yace, wannan ba abune da za'a amince dashi ba.
Yace kwana daya kamin jana'izar sojojin shugaba Buhari ya ajiye dimbin aikin dake gabanshi ya tara 'yan fim aka yi sharholiya amma ya kasa halartar jana'izar sojoji wannan abin takaicine babba.
Yace yana girmama harkar fim kuma a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa ya bayar da gudummawarshi akai da kuma da yake zaman kanshi amma abin takaicine ace ana da lokacin nishadi amma ba'a da lokacin girmama masu bamu tsaron kasa.