A can baya an samu matar da ta haifi jariri da carbi a wuya a jahar Bauchi.
Kwatsam a satin da mu ke cikin nan SARAUNIYA ta samu labarin wata mata mai suna Aishatu a unguwar Kagarawal a jahar Gombe ta haifi jariri rataye da carbi a wuya a asibitin gwamnatin jahar (specialist hospital).
Mahaifiyar jaririn ta shaida wa SARAUNIYA yaron ya haura watanni sha biyar kafin a haifeshi. An kuma haifeshi makale da carbi a wuya.
Iyalen gaba daya sun bayyana wannan karuwa a matsayin wata falala da Allah ya saukar wa zuri'arsu. Yaro da mahaifiyarshi suna cikin koshin lafiya.