Rabiu Musa Kwankwaso, daya daga cikin jiga jigan jam'iyyar APC wanda ke ware kanshi daga jam'iyyar mai mulki, yace za a kada shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 mai tunkarowa.
Ya bayyana jam'iyyar PDP a matsayin jam'iyyar da tafi adawa da APC kuma mai karfin kayar da shugaban kasan a zaben mai zuwa, wanda za a yi a watan Fabrairu mai zuwa.
Ya kara da cewa, shine Dan takara mafi cancanta da zai iya rike tutar jam'iyyar kuma yaci zaben shugabancin kasar.
Kwankwaso, Sanata ne mai ci a yanzu kuma tsohon gwamnan jihar Kano, yana yawan ikirarin cewa da taimakon shi Buhari ya samu kuri'u miliyan 1.9 a jihar tashi. Ya kuma taimakawa gwamna Umar Ganduje, mataimakin shi a lokacin da ya rike Gwamnatin jihar, cin zaben 2015.
Wannan sukar jam'iyyar APC ta fito ne bayan kwanaki kadan bayan da yaki halartar zaben jam'iyyar da akayi a Abuja. Wannan ya faru ne sakamakon fadan da ke tsakanin magoya bayan shi da na gwamna Ganduje, wanda duk haduwar su sai sun raba abin fadi.
Daga : Naij Hausa