Babu Abinda Kiristanci Ya Tsinanamin, Inji 'Yar Tsohon Gomnan Oyo.
Sananniyar 'yar jaridar nan me yawan jawo cece-kuce kuma diya a gurin
tsohon gwamnan jihar Oyo, Kemi Olunloyo ta bayyana sha'awarta da shiga
addinin musulunci, tace babu abinda addinin kiristanci da take kanshi a
yanzu ya jawo mata banda dimuwa da rudani.
Kemi ta bayyana hakane a wani rubutu da tayi a dandalinta na sada
Zumunta da muhawara inda ta sanya hotunan ta sanye da Hijabi sannan ta
rubuta cewa:
Kwanannan zata karbi addinin musulunci, kuma a da ta kasance tare da
kakarta wadda ta rasu tana da shekaru dari da biyu a Duniya, makarantar
da take zuwa kusa da gidan kakartane shi yasa ta koma can da zama, su
kanyi sallah sau biyar a rana ba sau daya a sati ba kamar yanda take yi
tare da shaidanun mutane yanzu ba, tace, suna shagulgulan sallah babba
da karama tare.
Tace Musulunci addinine na zama lafiya kuma a cikinshine zata samu nutsuwa.
Ta dai karkare zancenta da cewa, yanzu babu ruwanta da addinin
kiristanci, dan kuwa babu abinda ya tsinana mata a rayuwa banda rudani,
musulunci zata koma kuma duk wanda baya son addinin musulunci sai ya
dena bibiyarta da lamurranta, komai yana da lokaci dama, yanzu dai ta
tabbata cewa a addinin musuluncine zata samu nutsuwar da take nema.