Da gaske ne Rarara ya ci Kudin Mawaka?
MAI DOKAR BARCI
Rarara Mai Zagin Barayin Gwamnati, Ya Yi Sama Da Fadi Da Sama Da Naira Milyan 100 Na Kungiyar Mawaka
Sanin kowa ne mawaki Dauda Kahutu Rarara ya kware wajen yin hannun ka mai sanda a duk lokacin da aka ce an zargi wani jigo na jam'iyyar adawa da wawushe dukiyar kasa, inda yake fitar da sabuwar waka kan wanda ake zargi da handame dukiyar kasan.
Saidai a yanzu halin da mawakin ke ciki kan zarginsa da ake yi na yin sama da fadi da kudin kungiyar mawakan Arewa wato AMFO, za mu iya cewa mai dokar bacci ya buge da gyangyadi.
Kungiyar dai tana zargin Rarara ne da yin sama da fadinda sama da naira milyan 100 wanda kungiyar gwamnonin Arewa ta ba su.
Rahotanni sun nuna cewa mawaki Rarara ya gina filin kwallo ne a kauyen su Kahutu dake jihar Katsina, sannan kuma ya kafa makarantar kwallo wanda ake zargin duk da kudin kumgiyar ta mawakan ya gina.
Haka kuma wata majiya ta kara da cewa ko lokacin da Gwamna Masari ya ga katafaren filin kwallon da Rararan ya gina, sai da ya kwabe shi kan yadda aka yi ya samu kudin gina irin wannan fili.
Daya daga cikin mawakan da aka yi fadi tashi da shi wajen kare martabar APC, Abubakar Sani ya bayyanawa RARIYA cewa kusan mawaka dari biyar da suka bada gudummawa wajen nasarar gwamnatin APC wadanda suke amfana da gwamnatin ba su fi mutum biyu zuwa uku ba.
Abubakar Sani ya kara da cewa dama ya tabbatar da cewa irin wannan ranar tana nan tafe, ya san da cewa akwai wadanda suke amfani da suna mawakan APC suna cin kudi.
"Idan ka duba da yawa daga cikin mawakan da aka yi wakar "Lema Ta Yage"da su, duk sun dawo daga rakiyar Rarara saboda yadda yake amfani da sunansu yana bin manyan jiga-jigan APC yana karbar kudi".
Abubakar Sani ya kara da cewa wani kuskure da aka samu kan badakar kudin shine rashin samarwa kungiyar asusun ajiya, inda Rararan ya dinga amfani da asusun ajiyarsa wajen ajiye kudin.
Shugaban kungiyar mawakan na yankin Arewa Haruna Aliyu Ningi dake jihar Bauchi ya bayyanawa manema labarai cewa yace Gwamnan jihar Zamfara ya ba su kudin bayan sun bukaci hakan kan irin gudummawar da suka bayar a yayin zabukan 2015, kuma sun shirya bayar da gagarumar gudummawa a zabukan 2019 dake tafe.
Tunda farko Dauda Rarara shiya shige gaba wajen karbo kudaden kuma ya tabbatar mun da cewar Gwamnan Jihar Zamfara AbdulAziz Yari ya fara basu nera Milyan Sittin sai dai wadanda suka yi hanya har aka bayar da kudaden ya ba su nera milyan goma sha takwas kamar yadda Haruna Ningi ya kara da bayyanawa.
Ya kara da cewar "a matsayina na shugaban kungiya har zuwa yau Rarara bai taba yi mun maganar ba, bayan lokacin da na sake tuntubar sa, sai yace har yanzu ba a cika ragowar kudaden ba, amma na kusa da shi wanda shi ma yana daga cikin mawakan mai suna Isiyaku Oris yace tuni an baiwa Rarara ragowar nera milyan arba'in din.
"A hakan dai muka bukaci nera milyan arba'in da biyu da suka rage a hannun shi ya kawo su a zo a zauna a tattauna a kan su sai yace wai asusun ajiyar sa na banki ya sami matsala".
Manazarta dai na ganin cewa tun bayan da mawakin ya yi wakar habaici ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso farin jininsa ya soma raguwa, inda ko ya yi sabuwar waka ba ta tasiri kamar a baya.
Har ya zuwa yanzu dai mawaƙin bai ce komai ba, game da zargin da ake yi masa. Sai dai ana tunanin da ya dawo daga aikin Umarar da ya tafi zai maida raddi a kan maganar, walau ta hanyar kare kan sa a kafafen watsa labarai ko kuma ta fannin waka.
Daga:
Aliyu Ahmed
Da:
Rumbunkannywood