Zuwa Ga Masu Ilimin Kimiya 1

A yau acikin duniya akwai musulmi sama da mutan mikiyan dari tara wadanda babu wata wata sun kar6a kuma suna amince Alqur'ani maganar Allah ne kuma gagara koyo ne.to me ze hana ma su amince?tunda hatta makiyan musulunci sunyi magana akan mu+ujuzancin Alqur'ani.Rev.R. Bosworth-Smith a cikin littafinsa wanda yasa masa suna:Muhammad and Muhammadanism,ya fadi raayinsa akan Alqur'ani cewa 'Mu+ujuzan tsarki da tsarki ne,na hikima kuma da gaskiya,wani bature kuma da ake ce masa A.J Arberry a cikin gabatarwan sa na tafsirin kur'ani da yayi yace:
'duk lokacin danake jin karatun kur'ani sai inji kamar ina sauraron zakin tsarkiya ne,wadda karkashinta akwai wani salo mai sauti,da'iman,kamar bugun ganga watau dai kamar bugun zuciyata'
daga cikin wadannan kalmomi kuma sauran dake cikin gabatarwarsa sai aji kamar musulmi ne shi,amma yamutu yana bin tafarkin masihiyya.
Kuma wani mutumin britaniya mai suna Marmaduke Pichall,acikin gabatarwan tafsirin ya bayyana Alqur'ani da cewa'shi gagara koyon salo ne,wadda sautinsa yake motsa zukata zuwa ga hawaye da murna'shi wannan mutum ya rubgumi musulunci ne kafin yayi tafsirin Kur'ani,amma bazamu iya tabbatarwa da cewa ko yanada wannan raayi ne gabanin ko bayan musuluntarsa ba,duk ma yadda lamarin yake daida yawa cikin musulmi da wadanda ba musulmi ba,sun bada yabon su na hakika akan wahayin karshe watau Alku'ani,sahabban Annabi s.a.w sunga kyau da zati da girman kira da karamcin sakon Allah,duk da wadannan yabe-yabe dashaidu,bijirarre da mai shakka yace wadannan duk ra'ayi ne kawai kurum.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post