Wata rana wani Bahaushe wai shi Wawa za shi
fatauci, sai ya bi ta kasar Yarbawa, Wawa ba ya
jin Yarbanci, mutanen da ya tarar a wannan gari
su kuma ba su jin Hausa. Amma duk da wannan
Wawa bai lura ba. Yana cikin tafiya, ya kawo
kofar gari, sai ya ga wani katon garken shanu fari
fat suna kiwo. Wawa ya yi mamakin wanda ke da
wadannan shanu masu yawa haka, sai ya
tambayi wani mutum nan kofa ya gaya masa ko
shanun wane ne wadannan.
Mutumin ya amsa da Yarbanci, ya ce, “Ni ban ji
ba.”
Wawa da ya ji haka tsammani ya ke “Ni ban ji
ba” shi ne mutumin da ke da shanun. Don haka
ya ce, “Ni-ban-ji=ba lalle yana da sukuni.” Ya
wuce ya shiga gari, sai ya kai ga wani babban
gida. Ya daga kai, ya ga lalle gidan nan ya amsa
sunansa, samari, wa ke da wannan babban gida
haka?”
Yaron ba ya jin Hausa, shi kuma sai ya ce a cikin
harshensa “Ni ban ji ba.”
Da Wawa ya ji haka, sai ya ce, “Kai, ba shakka
Ni-ban-ji-ba ba wanda ya fi shi sule garin nan.
Wannan irin gida sai ka ce na Sarki. Da ganin
wannan ai ko ba a gaya maka ba ka san wurin
nan sule ya zauna da gindinsa.” Ya haura
takalmansa ya wuce faram, faram, faram, faram,
har bakin kogin garin. Yana zuwa sai ya tarad da
wani jirgi ya zo, ana ta fid da kaya daga cikinsa.
Wawa ya dubi kaya, ya ce, “Oi! Wannanjirgi ya
yiwo kaya!” Ya dubi wani nan kusa gare shi, ya
ce, “Dan’uwa, duk ko kayan nan na mutum guda
ne?”
Shi bayarabe bai ji abin da ya ce ba, sai ya dube
shi, ya ce, “Ni ban ji ba.”
Da Wawa ya ji haka sai ya rike baki, ya ce, “masu
gari! Hakika Ni-ban-ji-ba ya huce haushinsa. Ina
ma Allah zai sa in gamu da wannan mutum, ko
wajen adonsa ma in more ma idona!” Sai ya
zauna ya huta, ya debi ruwa ya sha, ya kama
hanya zai wuce. Ya kai kofar gari ke nan, sai ya
ga wani mattacce an dauko shi, za a kai shi a
rufe, wadansu na ta kuka. Wawa ya tsaya yana
dubansu. Tausai ya kama shi, ya matsa wajen
wata tsohuwa, ya ce mata, “Wane ne wannan ya
riga mu gidan gaskiya?”
Tsohuwa ba ta ji Hausa ba, sai ta dube shi, ta ce,
“Ni ban ji ba.”
Wawa da ya ji haka sai ya daffe kai, ya ce, “Allah
mai girma! Ka san kowa samun nan na duniya ya
ruda, ya shiga uku. Don Allah dubi abin da Ni-
ban-ji-ba ya tara. Ga shi yanzu ya zama sai
labari, kamar dadai duniya ba a halicce shi ba!
Cikin duk abin nan da ya tara, dubi dan kyallen da
za a kai shi da shi. Tun da ya ke al’amarin nan
haka ya ke, to, ni yanzu me ya ruda ni har da na
rabo da gida don rashin wadar zuci? Ga shi Allah
bai hana mini abin da zan ci ba. Watau ba dai
abin da ya fid da ni gida sai in sami abin alfahari
in kara sabo. Mhm, Allah ya kiyashe mu da aikin
Shaidan! Na gode Allah da ya kawo ni nan na
sami gargadi daga al’amarin Ni-ban-ji-ba. Ba
sauran abin da ya fi, sai in koma garimmu, in
dangana da abin da Allah ke ba ni wajen ‘yar
gonata.
Da ma an ce, “Gani ga wani ya isa tsoron Allah.”
Musa ya tashi, har ya bude zauren farko, sai ya ji
bayi sun farka. Sai ya kuta, ya koma.
Da Waziri ya ga kwana biyu sun wuce, kowace
safiya bayin nan da ya sa suka dawo sai su ce
ba wanda ya ko leko zauren, har abin ya dame
shi, ya ce, “A’a! Da ko na yi tsammanin zai fito,
dabara.” Ya kira wata tsohuwar baisarsa, ya
bayyana mata abin da ya ke so duka game da
Musa, ya ce mata in ta yi kokarin ta taimake shi
har ta sa Musa ya fita waje, zai ba ta fam goma,
ya kuma ‘yanta ta. Ya kawo sule goma, ya fara
ba ta ta lasa.
Tsohuwa ta ce, “Ta kwana gidan Sauki.”
Magariba na yi, sai ta shiga gidan Sarki da kayan
talla, ta kaikaici idon mutane ta yahuto Musa
waje guda, ta ce, “Mahmudu ya aiko ni, ya ce a
gaya maka wai kai haka za ka yarda ka lalace
cikin matia? Ya ce a gaya maka fa duniya ba ta
auren raggo.”
Musa ya matsa kusa da tsohuwa, ya ce, “Don
Allah iya, yana can yana ta yaki ko?”
Tsohuwa ta ce, “Habe! Yanzu sanisanimmu akwai
wanda a ke magana irin Mahmundu? Ni ma fa
can na ke sansani, mu ke yi musu abinci.
Mahmudu ya shaku da ni, ya aiko ni gare ka.”
Musa ya ce, “Koma maza ki gaya masa, gobe in
Allah ya so ya gan ni.” Tsohuwa ta koma.
Da dare ya yi, Musa ya saurara ya ji barci ya
kwashe bayin nan, sai ya shigo damaru, ya zo
wurin aku, ya ce, “Ka ji Mahmudu na can sansani
yana ta abin kirki, ni za sa in lalace nan cikin
mata.”
Aku ya ce, “Yallabai, ina ruwana? Ni ban hana ka
ba. Yaya barde kamarka zai ce za shi wurin yaki
a hana shi? Tun da ya ke niyyarka ka yi abin da
zai faranta wa tsohonka rai ne, ai kowane hadari
ka shiga Allah ya fisshe ka, yadda ya fid da Auta
dan Sarkin noma daga namun jeji.”
Musa ya ce, “Wane rigima ta kai shi ga fadawa
hannun namun jeji?” Aku ya karba: