Zaben 2019 za'a yi shine tsakanin 'yan takara masu gaskiya da barayi>>Gwamna El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, Zaben shekarar 2019 me zuwa za'a yi shine tsakanin barayi da masu gaskiya.


Gwamnan ya bayyan hakane a wajan kaddamar da kwamitin yakin neman zabenshi na 2019, kamar yanda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ya kara da cewa babu abinda jam'iyyar PDP ta sani in banda satar dukiyar kasa, yace zaben 2019 zabene tsakanin masu gaskiya da barayin, tsakanin masu kishin kasa da wanda suka je Abuja suka rika satar dukiyar kasa.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post