Majalisar Dinkin Duniya ta amince da aiwatar da kudurin da Najeriya ta mika mata, kan tsaida 24 ga watan Janairu na kowace shekara, a matsayin ranar ilimi ta duniya.
Jakadan Najeriya na din-din-din a zauren majalisar Tijjani Bande, ya ce kasashe da dama sun bayyana goyon bayansu ga Najeriya dangane da kudurin.
Baki dayan kasashe 193 masu wakilai a zauren majalisar dinkin duniyar ne suka marawa kudurin Najeriyar baya wajen zama doka a wannan Litinin da ta gabata, ba tare da hamayya ko kauracewa kada kuri’an kan kudurin ba, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar NAN ya rawaito.
Kasashe da kuma hukumomin da suka taimakawa Najeriya, wajen ganin Kudurin ranar ilimin ta Duniya ya samu karbuwa, sun hada da Singapore, Qatar, da kuma Ireland, tare da hadin gwiwar hukumomin majalisar dinkin duniya na kyautata ilimi da kimiya da al'adu UNESCO da kuma Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar dinkin duniya UNICEF.
Bikin ranar Ilimi ta duniya a kowace ranar 24 ga watan Janairun zai soma ne daga shekara ta 2019 da ke shirin kunno kai.
A karshe kudurin ya fayyace cewa hukumar majalisar dinkin duniya dake kyautata ilimi da kimiya da al'adu wato UNESCO ce aka dorawa nauyin kula da tunatarwa da kuma shirya bikin ranar Ilimin ta duniya lura da cewa ita mafi kusanci wajen kula da fannin a tsakanin hukumomin zauren Majalisar.
RFIhausa.