Hukumomi a birnin Madina sun sanar da mutuwar mutum hudu a dalilin wani mamakon ruwan sama, inda wasu da dama kuma ruwan ya hana su fitowa.
Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito hukumar da ke kare fararen hula ta ce yara kanana biyu mai shekaru tara da shida na cikin wadanda suka mutun tare da wani mutum da wata budurwa.
Hukumar ta kuma ce ruwa ya shafe wasu gidaje da ke gabashin birnin na Madina kuma masu aikin ceto na can suna neman wadanda ruwan ya hana su fitowa.
Sannan hukumar ta ce ta sami bayanai 76 da ke cewa ruwan ya janyo matsalar wutar lantarki da lalacewar na'ura mai hawa saman bene da mutane.
Kakakin hukumar, Kanar Khaled Al-Johani, ya ce ruwan ya yi ambaliya a wasu wurare masu kwari na yankin.
"Muna kokarin cire baraguzai a kan manyan tituna da kuma tsane ruwan da ya kwanta," in ji shi.
Ya ce ruwan ya tsare wasu mutum 40 a Rabigh, amma an ceto dukkansu.
A birnin Makkah ma an sami irin wannan ruwan saman, wanda ya bayyana rashin ingancin wasu hanyoyi da magudanan ruwa da aka gina a birnin.
Majalisar karamar hukumar ta Makkah ta yi barazanar kai karar ofishin shugaban karamar hukumar saboda rashin ingancin aiki.
Mataimakin shugaban majalisar, Fahd Al-Rouqi ya bayyana rashin jin dadinsa, inda ya nemi hukumar yaki da cin hanci da rashawa (Nazaha) ta binciki jami'an da ke da hannu wajen gina magudanan ruwan da hanyoyin marasa inganci.
Ya kara da cewa: "Ya kamata a tuhumi wadanda suka yi wannan aikin, kuma a hukunta su idan an same su da laifi."
BBChausa.